Ash-Shams

الشمس

The Sun15 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلشَّمۡسِ وَضُحَىٰهَا﴿١

1Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

وَٱلۡقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا﴿٢

2Kuma da wata idan ya bi ta.

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا﴿٣

3Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰهَا﴿٤

4Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا﴿٥

5Da sama da abin da ya gina ta.

وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا طَحَىٰهَا﴿٦

6Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

وَنَفۡسٖ وَمَا سَوَّىٰهَا﴿٧

7Da rai da abin da ya daidaita shi.

فَأَلۡهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقۡوَىٰهَا﴿٨

8Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa.

قَدۡ أَفۡلَحَ مَن زَكَّىٰهَا﴿٩

9Lalle ne wanda ya tsarkake[1] shi (rai) ya sãmi babban rabo.

وَقَدۡ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا﴿١٠

10Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe[1] shi (da laifi) ya tãɓe.

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِطَغۡوَىٰهَآ﴿١١

11Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشۡقَىٰهَا﴿١٢

12A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

فَقَالَ لَهُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقۡيَٰهَا﴿١٣

13Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمۡدَمَ عَلَيۡهِمۡ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمۡ فَسَوَّىٰهَا﴿١٤

14Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

وَلَا يَخَافُ عُقۡبَٰهَا﴿١٥

15Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

RELATED SURAHS