الليل
The Night • 21 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
2Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
3Da abin da ya halitta namiji da mace.
4Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
5To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
6Kuma ya gaskata kalma[1] mai kyãwo.
7To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
8Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
9Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
10To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
11Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
12Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya.
13Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
14Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
15Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa
16Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
17Kuma mafi taƙawa[1] zai nisance ta.
18Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
19Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
20Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
21To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).