Al-Ma'un

الماعون

The Small Kindnesses7 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ﴿١

1Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?

فَذَٰلِكَ ٱلَّذِي يَدُعُّ ٱلۡيَتِيمَ﴿٢

2To, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).

وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ﴿٣

3Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.

فَوَيۡلٞ لِّلۡمُصَلِّينَ﴿٤

4To, bone yã tabbata ga masallata.

ٱلَّذِينَ هُمۡ عَن صَلَاتِهِمۡ سَاهُونَ﴿٥

5Waɗan da suke masu shagala daga sallar su.

ٱلَّذِينَ هُمۡ يُرَآءُونَ﴿٦

6Waɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)

وَيَمۡنَعُونَ ٱلۡمَاعُونَ﴿٧

7Kuma suna hana taimako.

RELATED SURAHS