الضحى
The Morning Hours • 11 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Inã rantsuwa da hantsi.
2Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
3Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
4Kuma lalle ta ƙarshe[1] ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
5Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
6Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
7Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
8Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
9Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
10Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
11Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).