Ash-Sharh

الشرح

The Relief8 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ﴿١

1Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?

وَوَضَعۡنَا عَنكَ وِزۡرَكَ﴿٢

2Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.

ٱلَّذِيٓ أَنقَضَ ظَهۡرَكَ﴿٣

3Wanda ya nauyayi bãyanka?

وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ﴿٤

4Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?

فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا﴿٥

5To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرٗا﴿٦

6Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ﴿٧

7Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).

وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب﴿٨

8Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.

RELATED SURAHS