At-Tin

التين

The Fig8 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيۡتُونِ﴿١

1Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.[1]

وَطُورِ سِينِينَ﴿٢

2Da Dũr Sĩnĩna.[1]

وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ﴿٣

3Da wannan gari[1] amintacce.

لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِيٓ أَحۡسَنِ تَقۡوِيمٖ﴿٤

4Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.

ثُمَّ رَدَدۡنَٰهُ أَسۡفَلَ سَٰفِلِينَ﴿٥

5Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ﴿٦

6Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.

فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّينِ﴿٧

7To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?

أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَٰكِمِينَ﴿٨

8Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?[1]

RELATED SURAHS