Al-'Alaq

العلق

The Clot19 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ﴿١

1Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ﴿٢

2Ya hahitta mutum daga gudan jini.

ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ﴿٣

3Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.

ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ﴿٤

4Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.

عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ﴿٥

5Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

كَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ﴿٦

6A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).

أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ﴿٧

7Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.

إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ﴿٨

8Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.

أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ﴿٩

9Shin, kã ga wanda ke hana.

عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ﴿١٠

10Bãwã idan yã yi salla?

أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ﴿١١

11Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?

أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ﴿١٢

12Ko ya yi umurni da taƙawa?

أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ﴿١٣

13Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?

أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ﴿١٤

14Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?

كَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ﴿١٥

15A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.

نَاصِيَةٖ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٖ﴿١٦

16Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.

فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ﴿١٧

17Sai ya kirayi ƙungiyarsa.

سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ﴿١٨

18Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).

كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩﴿١٩

19A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,[1] kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).

RELATED SURAHS