الحجر
The Rocky Tract • 99 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
2Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.[1]
3Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.
4Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
5Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
6Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."
7"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"
8Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,[1] bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
9Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.
10Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka.
11Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
12Kamar wancan ne Muke shigar da shi[1] a cikin zukãtan mãsu laifi.
13Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige[1] .
14Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
15Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."
16Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
17Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
18Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
19Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.
20Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã[1] da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
21Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
22Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.
23Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.
24Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
25Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
26Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
27Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar[1] iskar zafi.
28Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."
29"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa[1] a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
30Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
31Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.
32Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"
33Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."
34Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."
35"Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."
36Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."
37Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
38"Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne."
39Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."
40"Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."
41Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."
42"Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."
43Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya.
44Tanã da ƙõfõfi bakwai,[1] ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.
45Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
46"Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."
47Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
48Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba.
49Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
50Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi.
51Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.
52A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."
53Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."
54Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra[1] ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
55Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
56Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu?"
57Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"
58Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."
59"Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
60"Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
61To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,
62Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."
63Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."
64"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
65"Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."
66Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba.
67Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
68Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."
69"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
70Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"
71Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna[1] idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
72Rantsuwa da[1] rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
73Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
74Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
75Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
76Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.[1]
77Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
78Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika[1] sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
79Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
80Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri[1] sun ƙaryata Manzanni.
81Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
82Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
83Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba.
84Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
85Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
86Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
87Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu[1] da Alƙur'ãni mai girma.
88Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
89Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne."
90Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,[1]
91Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.
92To, rantsuwa da Ubangijinka![1] Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
93Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
94Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
95Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu[1] izgili.
96Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.
97Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
98Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
99Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.