القدر
The Power • 5 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
2To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?
3Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
4Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
5Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.