Ar-Rahman

الرحمن

The Most Merciful78 ayahsMedinan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱلرَّحۡمَٰنُ﴿١

1(Allah) Mai rahama.

عَلَّمَ ٱلۡقُرۡءَانَ﴿٢

2Yã sanar da Alƙur'ani.

خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ﴿٣

3Yã halitta mutum.

عَلَّمَهُ ٱلۡبَيَانَ﴿٤

4Yã sanar da shi bayãni (magana).

ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ بِحُسۡبَانٖ﴿٥

5Rãnã da watã a kan lissãfi suke.

وَٱلنَّجۡمُ وَٱلشَّجَرُ يَسۡجُدَانِ﴿٦

6Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.

وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلۡمِيزَانَ﴿٧

7Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.

أَلَّا تَطۡغَوۡاْ فِي ٱلۡمِيزَانِ﴿٨

8Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.

وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ﴿٩

9Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.

وَٱلۡأَرۡضَ وَضَعَهَا لِلۡأَنَامِ﴿١٠

10Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.

فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَٱلنَّخۡلُ ذَاتُ ٱلۡأَكۡمَامِ﴿١١

11A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.

وَٱلۡحَبُّ ذُو ٱلۡعَصۡفِ وَٱلرَّيۡحَانُ﴿١٢

12Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿١٣

13To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku [1]kuke ƙaryatãwa?

خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ كَٱلۡفَخَّارِ﴿١٤

14Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.

وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٖ مِّن نَّارٖ﴿١٥

15Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿١٦

16To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ وَرَبُّ ٱلۡمَغۡرِبَيۡنِ﴿١٧

17Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿١٨

18To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ يَلۡتَقِيَانِ﴿١٩

19Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.

بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٞ لَّا يَبۡغِيَانِ﴿٢٠

20A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٢١

21To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

يَخۡرُجُ مِنۡهُمَا ٱللُّؤۡلُؤُ وَٱلۡمَرۡجَانُ﴿٢٢

22Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٢٣

23To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

وَلَهُ ٱلۡجَوَارِ ٱلۡمُنشَـَٔاتُ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ﴿٢٤

24Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٢٥

25To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

كُلُّ مَنۡ عَلَيۡهَا فَانٖ﴿٢٦

26Dukkan wanda ke kanta[1] mai ƙãrẽwa ne.

وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ﴿٢٧

27Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٢٨

28To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

يَسۡـَٔلُهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ كُلَّ يَوۡمٍ هُوَ فِي شَأۡنٖ﴿٢٩

29wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٣٠

30To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

سَنَفۡرُغُ لَكُمۡ أَيُّهَ ٱلثَّقَلَانِ﴿٣١

31Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ [1]mãsu nauyin halitta biyu!

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٣٢

32To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ إِنِ ٱسۡتَطَعۡتُمۡ أَن تَنفُذُواْ مِنۡ أَقۡطَارِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ فَٱنفُذُواْۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلۡطَٰنٖ﴿٣٣

33Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٣٤

34To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

يُرۡسَلُ عَلَيۡكُمَا شُوَاظٞ مِّن نَّارٖ وَنُحَاسٞ فَلَا تَنتَصِرَانِ﴿٣٥

35Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٣٦

36To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ وَرۡدَةٗ كَٱلدِّهَانِ﴿٣٧

37Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٣٨

38To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُسۡـَٔلُ عَن ذَنۢبِهِۦٓ إِنسٞ وَلَا جَآنّٞ﴿٣٩

39To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٤٠

40To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

يُعۡرَفُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ بِسِيمَٰهُمۡ فَيُؤۡخَذُ بِٱلنَّوَٰصِي وَٱلۡأَقۡدَامِ﴿٤١

41zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٤٢

42To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ﴿٤٣

43Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.

يَطُوفُونَ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَ حَمِيمٍ ءَانٖ﴿٤٤

44Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٤٥

45To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

وَلِمَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ جَنَّتَانِ﴿٤٦

46Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٤٧

47To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

ذَوَاتَآ أَفۡنَانٖ﴿٤٨

48Mãsu rassan itãce.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٤٩

49To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فِيهِمَا عَيۡنَانِ تَجۡرِيَانِ﴿٥٠

50A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٥١

51To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فِيهِمَا مِن كُلِّ فَٰكِهَةٖ زَوۡجَانِ﴿٥٢

52A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٥٣

53To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ فُرُشِۭ بَطَآئِنُهَا مِنۡ إِسۡتَبۡرَقٖۚ وَجَنَى ٱلۡجَنَّتَيۡنِ دَانٖ﴿٥٤

54Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٥٥

55To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فِيهِنَّ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ﴿٥٦

56A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٥٧

57To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

كَأَنَّهُنَّ ٱلۡيَاقُوتُ وَٱلۡمَرۡجَانُ﴿٥٨

58Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٥٩

59To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

هَلۡ جَزَآءُ ٱلۡإِحۡسَٰنِ إِلَّا ٱلۡإِحۡسَٰنُ﴿٦٠

60Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٦١

61To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ﴿٦٢

62Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٦٣

63To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

مُدۡهَآمَّتَانِ﴿٦٤

64Mãsu duhun inuwa.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٦٥

65To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فِيهِمَا عَيۡنَانِ نَضَّاخَتَانِ﴿٦٦

66A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٦٧

67To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فِيهِمَا فَٰكِهَةٞ وَنَخۡلٞ وَرُمَّانٞ﴿٦٨

68A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٦٩

69To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

فِيهِنَّ خَيۡرَٰتٌ حِسَانٞ﴿٧٠

70A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyawun hãlãye, mãsu kyaun halitta.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٧١

71To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

حُورٞ مَّقۡصُورَٰتٞ فِي ٱلۡخِيَامِ﴿٧٢

72Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٧٣

73To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ﴿٧٤

74Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٧٥

75To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ رَفۡرَفٍ خُضۡرٖ وَعَبۡقَرِيٍّ حِسَانٖ﴿٧٦

76Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ﴿٧٧

77To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?

تَبَٰرَكَ ٱسۡمُ رَبِّكَ ذِي ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ﴿٧٨

78Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.

RELATED SURAHS