Al-Waqi'ah

الواقعة

The Event96 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ﴿١

1Idan mai aukuwa ta auku.

لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ﴿٢

2Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.

خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ﴿٣

3(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.

إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا﴿٤

4Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.

وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا﴿٥

5Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.

فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا﴿٦

6Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.

وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ﴿٧

7Kuma kun kasance nau'i uku.

فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ﴿٨

8Watau mazõwa dãma[1]. Mẽne ne mazõwa dãma?

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ﴿٩

9Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?

وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلسَّٰبِقُونَ﴿١٠

10Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,

أُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ﴿١١

11Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.

فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ﴿١٢

12A ckin Aljannar ni'ima.

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿١٣

13Jama'a ne daga mutãnen farko.[1]

وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ﴿١٤

14Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.

عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ﴿١٥

15(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.

مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ﴿١٦

16Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.

يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ﴿١٧

17Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.

بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ﴿١٨

18Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.

لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ﴿١٩

19Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.

وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ﴿٢٠

20Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.

وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ﴿٢١

21Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.

وَحُورٌ عِينٞ﴿٢٢

22Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.

كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ﴿٢٣

23Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.

جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ﴿٢٤

24A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.

لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا﴿٢٥

25Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.

إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا﴿٢٦

26Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ﴿٢٧

27Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ﴿٢٨

28(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.

وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ﴿٢٩

29Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.

وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ﴿٣٠

30Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.

وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ﴿٣١

31Da wani ruwa mai gudãna.

وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ﴿٣٢

32Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.

لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ﴿٣٣

33Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.

وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ﴿٣٤

34Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.

إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ﴿٣٥

35Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.

فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا﴿٣٦

36Sa'an nan Muka sanya su budurwai.

عُرُبًا أَتۡرَابٗا﴿٣٧

37Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.

لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ﴿٣٨

38Ga mazõwa dãma.

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿٣٩

39Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.

وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ﴿٤٠

40Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.

وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ﴿٤١

41Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?

فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ﴿٤٢

42Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.

وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ﴿٤٣

43Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.

لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ﴿٤٤

44Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.

إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ﴿٤٥

45Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.

وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ﴿٤٦

46Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.

وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ﴿٤٧

47Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ﴿٤٨

48"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"

قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ﴿٤٩

49Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."

لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ﴿٥٠

50"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."

ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ﴿٥١

51"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"

لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ﴿٥٢

52"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."

فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ﴿٥٣

53"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."

فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ﴿٥٤

54"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."

فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ﴿٥٥

55"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."

هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ﴿٥٦

56Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.

نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ﴿٥٧

57Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?

أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ﴿٥٨

58Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?

ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ﴿٥٩

59Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?

نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ﴿٦٠

60Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa[1] ba,

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ﴿٦١

61A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.

وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ﴿٦٢

62Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?

أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ﴿٦٣

63Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?

ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّٰرِعُونَ﴿٦٤

64Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?

لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ﴿٦٥

65Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.

إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ﴿٦٦

66(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"

بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ﴿٦٧

67"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ﴿٦٨

68Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?

ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ﴿٦٩

69Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?

لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ﴿٧٠

70Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ﴿٧١

71Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?

ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ﴿٧٢

72Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?

نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ﴿٧٣

73Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ﴿٧٤

74Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.

۞ فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ﴿٧٥

75To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.

وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ﴿٧٦

76Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.

إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ﴿٧٧

77Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.

فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ﴿٧٨

78A cikin wani littafi tsararre.

لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ﴿٧٩

79Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.

تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿٨٠

80Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.

أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ﴿٨١

81Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?

وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ﴿٨٢

82Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?

فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ﴿٨٣

83To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).

وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ﴿٨٤

84Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.

وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ﴿٨٥

85Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.

فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ﴿٨٦

86To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?

تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ﴿٨٧

87Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.[1]

فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ﴿٨٨

88To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,

فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ﴿٨٩

89Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ﴿٩٠

90Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,

فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ﴿٩١

91Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ﴿٩٢

92Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,

فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ﴿٩٣

93Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.

وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ﴿٩٤

94Da ƙõnuwa da Jahĩm,

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ﴿٩٥

95Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ﴿٩٦

96Sabõda haka, ka tsarkake[1] sũnan Ubangijinka, Mai karimci.

RELATED SURAHS