Al-Qamar

القمر

The Moon55 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ﴿١

1Sã'a ta yi kusa, kuma wata [1]ya tsãge.

وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ﴿٢

2Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"

وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ﴿٣

3Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.

وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ﴿٤

4Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.

حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ﴿٥

5Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.

فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡۘ يَوۡمَ يَدۡعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَيۡءٖ نُّكُرٍ﴿٦

6Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.

خُشَّعًا أَبۡصَٰرُهُمۡ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ كَأَنَّهُمۡ جَرَادٞ مُّنتَشِرٞ﴿٧

7¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.

مُّهۡطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِۖ يَقُولُ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَسِرٞ﴿٨

8Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"

۞ كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ﴿٩

9Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.

فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَغۡلُوبٞ فَٱنتَصِرۡ﴿١٠

10Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."

فَفَتَحۡنَآ أَبۡوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٖ مُّنۡهَمِرٖ﴿١١

11Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.

وَفَجَّرۡنَا ٱلۡأَرۡضَ عُيُونٗا فَٱلۡتَقَى ٱلۡمَآءُ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ قَدۡ قُدِرَ﴿١٢

12Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi.

وَحَمَلۡنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلۡوَٰحٖ وَدُسُرٖ﴿١٣

13Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.

تَجۡرِي بِأَعۡيُنِنَا جَزَآءٗ لِّمَن كَانَ كُفِرَ﴿١٤

14Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.

وَلَقَد تَّرَكۡنَٰهَآ ءَايَةٗ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ﴿١٥

15Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ﴿١٦

16To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na?

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ﴿١٧

17Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

كَذَّبَتۡ عَادٞ فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ﴿١٨

18Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na?

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِي يَوۡمِ نَحۡسٖ مُّسۡتَمِرّٖ﴿١٩

19Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.

تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٖ مُّنقَعِرٖ﴿٢٠

20Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ﴿٢١

21To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na?

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ﴿٢٢

22Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ﴿٢٣

23Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.

فَقَالُوٓاْ أَبَشَرٗا مِّنَّا وَٰحِدٗا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٍ﴿٢٤

24Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.

أَءُلۡقِيَ ٱلذِّكۡرُ عَلَيۡهِ مِنۢ بَيۡنِنَا بَلۡ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٞ﴿٢٥

25"Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"

سَيَعۡلَمُونَ غَدٗا مَّنِ ٱلۡكَذَّابُ ٱلۡأَشِرُ﴿٢٦

26Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?

إِنَّا مُرۡسِلُواْ ٱلنَّاقَةِ فِتۡنَةٗ لَّهُمۡ فَٱرۡتَقِبۡهُمۡ وَٱصۡطَبِرۡ﴿٢٧

27Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar[1] ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.

وَنَبِّئۡهُمۡ أَنَّ ٱلۡمَآءَ قِسۡمَةُۢ بَيۡنَهُمۡۖ كُلُّ شِرۡبٖ مُّحۡتَضَرٞ﴿٢٨

28Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.

فَنَادَوۡاْ صَاحِبَهُمۡ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ﴿٢٩

29Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ﴿٣٠

30To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na?

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَكَانُواْ كَهَشِيمِ ٱلۡمُحۡتَظِرِ﴿٣١

31Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ﴿٣٢

32Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطِۭ بِٱلنُّذُرِ﴿٣٣

33Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٖۖ نَّجَّيۡنَٰهُم بِسَحَرٖ﴿٣٤

34Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.

نِّعۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَن شَكَرَ﴿٣٥

35Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.

وَلَقَدۡ أَنذَرَهُم بَطۡشَتَنَا فَتَمَارَوۡاْ بِٱلنُّذُرِ﴿٣٦

36Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin.

وَلَقَدۡ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيۡفِهِۦ فَطَمَسۡنَآ أَعۡيُنَهُمۡ فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ﴿٣٧

37Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na."

وَلَقَدۡ صَبَّحَهُم بُكۡرَةً عَذَابٞ مُّسۡتَقِرّٞ﴿٣٨

38Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.

فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ﴿٣٩

39To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na.

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ﴿٤٠

40Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

وَلَقَدۡ جَآءَ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ ٱلنُّذُرُ﴿٤١

41Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.

كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ﴿٤٢

42Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.

أَكُفَّارُكُمۡ خَيۡرٞ مِّنۡ أُوْلَٰٓئِكُمۡ أَمۡ لَكُم بَرَآءَةٞ فِي ٱلزُّبُرِ﴿٤٣

43Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?

أَمۡ يَقُولُونَ نَحۡنُ جَمِيعٞ مُّنتَصِرٞ﴿٤٤

44Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"

سَيُهۡزَمُ ٱلۡجَمۡعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ﴿٤٥

45Zã a karya[1] tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.

بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوۡعِدُهُمۡ وَٱلسَّاعَةُ أَدۡهَىٰ وَأَمَرُّ﴿٤٦

46Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.

إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٖ﴿٤٧

47Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.

يَوۡمَ يُسۡحَبُونَ فِي ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ ذُوقُواْ مَسَّ سَقَرَ﴿٤٨

48Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."

إِنَّا كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَٰهُ بِقَدَرٖ﴿٤٩

49Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.

وَمَآ أَمۡرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٞ كَلَمۡحِۭ بِٱلۡبَصَرِ﴿٥٠

50Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.

وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَآ أَشۡيَاعَكُمۡ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ﴿٥١

51Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?

وَكُلُّ شَيۡءٖ فَعَلُوهُ فِي ٱلزُّبُرِ﴿٥٢

52Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.

وَكُلُّ صَغِيرٖ وَكَبِيرٖ مُّسۡتَطَرٌ﴿٥٣

53Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّٰتٖ وَنَهَرٖ﴿٥٤

54Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.

فِي مَقۡعَدِ صِدۡقٍ عِندَ مَلِيكٖ مُّقۡتَدِرِۭ﴿٥٥

55A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.

RELATED SURAHS