At-Takwir

التكوير

The Overthrowing29 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ﴿١

1Idan rãna aka shafe haskenta

وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ﴿٢

2Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).

وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ﴿٣

3Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.

وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ﴿٤

4Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna[1] aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.

وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ﴿٥

5Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.

وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ﴿٦

6Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.

وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ﴿٧

7Kuma idan rãyuka aka haɗa[1] su da jikunkunansu.

وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ﴿٨

8Kuma idan wadda aka turbuɗe[1] ta da rai aka tambaye ta.

بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ﴿٩

9"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"

وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ﴿١٠

10Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ﴿١١

11Kuma idan sama aka fẽɗe ta.

وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ﴿١٢

12Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ﴿١٣

13Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ﴿١٤

14Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).

فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ﴿١٥

15To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã[1] ba.

ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ﴿١٦

16Mãsu gudu suna ɓũya.

وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ﴿١٧

17Da dare idan ya bãyar da bãya.

وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ﴿١٨

18Da sãfiya idan ta yi lumfashi.

إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ﴿١٩

19Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.

ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ﴿٢٠

20Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ﴿٢١

21Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ﴿٢٢

22Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ﴿٢٣

23Kuma lalle ne, yã gan shi[1] a cikin sararin sama mabayyani.

وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ﴿٢٤

24Kuma shi, ga gaibi[1] bã mai rowa ba ne.

وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ﴿٢٥

25Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.

فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ﴿٢٦

26Shin, a inã zã ku tafi?

إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ﴿٢٧

27Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.

لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ﴿٢٨

28Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.

وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿٢٩

29Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

RELATED SURAHS