'Abasa

عبس

He Frowned42 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ﴿١

1Yã game huska[1] kuma ya jũya bãya.

أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ﴿٢

2Sabõda makãho yã je masa.

وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ﴿٣

3To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ﴿٤

4Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ﴿٥

5Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.

فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ﴿٦

6Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ﴿٧

7To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ﴿٨

8Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

وَهُوَ يَخۡشَىٰ﴿٩

9Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ﴿١٠

10Kai kuma kã shagala ga barinsa!

كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ﴿١١

11A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ﴿١٢

12Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah).

فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ﴿١٣

13(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ﴿١٤

14Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ﴿١٥

15A cikin hannãyen mala'iku marubũta.

كِرَامِۭ بَرَرَةٖ﴿١٦

16Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.

قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ﴿١٧

17An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ﴿١٨

18Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ﴿١٩

19Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ﴿٢٠

20Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.

ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ﴿٢١

21Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ﴿٢٢

22Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.

كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ﴿٢٣

23Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ﴿٢٤

24To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.

أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا﴿٢٥

25Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.

ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا﴿٢٦

26Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.

فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا﴿٢٧

27Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.

وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا﴿٢٨

28Da inabi da ciyãwa.

وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا﴿٢٩

29Da zaitũni da itãcen dabĩno.

وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا﴿٣٠

30Da lambuna, mãsu yawan itãce.

وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا﴿٣١

31Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.

مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ﴿٣٢

32Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ﴿٣٣

33To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.

يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ﴿٣٤

34Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.

وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ﴿٣٥

35Da uwarsa da ubansa.

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ﴿٣٦

36Da mãtarsa da ɗiyansa.

لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ﴿٣٧

37Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ﴿٣٨

38Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.

ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ﴿٣٩

39Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.

وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ﴿٤٠

40Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.

تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ﴿٤١

41Baƙi zai rufe su.

أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ﴿٤٢

42Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

RELATED SURAHS