Al-Infitar

الانفطار

The Cleaving19 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ﴿١

1Idan sama ta tsãge.

وَإِذَا ٱلۡكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتۡ﴿٢

2Kuma idan taurãri suka wãtse.

وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ فُجِّرَتۡ﴿٣

3Kuma idan tẽkuna aka facce su.

وَإِذَا ٱلۡقُبُورُ بُعۡثِرَتۡ﴿٤

4Kuma idan kaburbura aka tõne su.

عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ وَأَخَّرَتۡ﴿٥

5Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلۡكَرِيمِ﴿٦

6Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.

ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ﴿٧

7Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ﴿٨

8A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

كَلَّا بَلۡ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ﴿٩

9A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

وَإِنَّ عَلَيۡكُمۡ لَحَٰفِظِينَ﴿١٠

10Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

كِرَامٗا كَٰتِبِينَ﴿١١

11Mãsu daraja, marubũta.

يَعۡلَمُونَ مَا تَفۡعَلُونَ﴿١٢

12Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ﴿١٣

13Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ ٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ﴿١٤

14Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

يَصۡلَوۡنَهَا يَوۡمَ ٱلدِّينِ﴿١٥

15Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

وَمَا هُمۡ عَنۡهَا بِغَآئِبِينَ﴿١٦

16Bã zã su faku daga gare ta ba.

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ﴿١٧

17Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?

ثُمَّ مَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ﴿١٨

18Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

يَوۡمَ لَا تَمۡلِكُ نَفۡسٞ لِّنَفۡسٖ شَيۡـٔٗاۖ وَٱلۡأَمۡرُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ﴿١٩

19Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

RELATED SURAHS