الزلزلة
The Earthquake • 8 ayahs • Medinan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
4A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
7To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.