العاديات
The Chargers • 11 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
2Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
3Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
4Sai su motsar da ƙũra game da shi.
5Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.
6Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
7Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.
8Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
9Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
10Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
11Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?