القارعة
The Striking Calamity • 11 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
2Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
3Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
4Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
5Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
6To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
7To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
8Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
9To, uwarsa Hãwiya ce.
10Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
11Wata wuta ce mai kuna.