التكاثر
The Rivalry in Worldly Increase • 8 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (daga ibada mai amfaninku).
2Har kuka ziyarci kaburbura.
3A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
4Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
5Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
6Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
7Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
8Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).