المطففين
The Defrauders • 36 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
2Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
3Kuma idan sun auna musu da zakka[1] ko da sikẽli, suna ragẽwa
4Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
5Domin yini mai girma.
6Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
7Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
8Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
9Wani ittãfi ne rubũtacce.
10Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
11Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
12Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
13Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
14A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
15A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
16Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
17Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
18A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
19Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
20Wani littãfi ne rubũtacce.
21Muƙarrabai[1] suke halarta shi.
22Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
23A kan karagu, suna ta kallo.
24Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
25Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
26¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
27Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
28(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
29Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
30Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
31Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
32Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
33Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
34To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
35A kan karagu, suna ta kallo.
36Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?[1]