الانشقاق
The Splitting Open • 25 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Idan sama ta kẽce,
2Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
3Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
4Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
5Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
6Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
7To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
8To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
9Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
10Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
11To, zã shi dinga kiran halaka!
12Kuma ya shiga sa'ĩr.
13Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
14Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
15Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
16To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
17Da dare, da abin da ya ƙunsa.
18Da watã idan (haskensa) ya cika.
19Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
20To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
21Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
22Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
23Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
24Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
25Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.