البروج
The Great Stars • 22 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
2Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,[1]
3Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta[1] a cikinsa
4An la'ani mutãnen rãmi.[1]
5Wato wuta wadda aka hura.
6A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
7Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
8Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
9Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
10Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
11Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
12Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
13Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
14Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
15Mai Al'arshi mai girma
16Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
17Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
18Fir'auna da samũdãwa?
19Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
20Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa).
21Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
22A cikin Allo tsararre.