الطارق
The Night Comer • 17 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
2To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
3Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.[1]
4Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
5To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
6An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
7Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
8Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
9Rãnar da ake jarrabawar asirai.
10Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
11Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
12Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa,[1]
13Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki[1]
14Kuma shĩ bã bananci[1] bane
15Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
16Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
17Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.