الصافات
Those Ranged in Ranks • 182 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
2Sa'an nan mãsu yin tsãwa[1] dõmin gargaɗi.
3Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
4Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
5Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
6Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
7Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
8Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
9Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
10Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
11Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
12Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
13Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
14Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
15Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
16"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
17"Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
18Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
19Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
20Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
21Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
22Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
23Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
24Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
25Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
26Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
27Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
28Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
29Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.
30"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
31"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
32"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
33To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
34Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
35Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
36Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
37Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
38Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
39Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
40Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
41Waɗannan sunã da abinci sananne.
42Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
43A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
44A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
45Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
46Farã mai dãɗi ga mashãyan.
47A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
48Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
49Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
50Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
51Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
52Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
53"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
54(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
55Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
56Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
57"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
58"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
59"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"
60Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
61Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
62Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
63Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
64Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
65Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
66To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
67Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
68Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
69Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
70Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
71Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
72Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
73Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
74Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
75Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
76Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
77Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
78Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.
79Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
80Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
81Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai.
82Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
83Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
84A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
85A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
86"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
87"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
88Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
89Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
90Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
91Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
92"Me ya sãme ku, bã ku magana?"
93Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
94Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
95Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
96"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
97Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
98Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
99Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
100"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
101Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro [1]mai haƙuri.
102To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."
103Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago
104Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"
105"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
106Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
107Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
108Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
109Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
110Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
111Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
112Kuma Muka yi masa bushãra[1] Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
113Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
114Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.
115Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
116Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
117Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
118Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
119Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
120Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
121Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
122Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai.
123Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
124A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
125"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
126"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"
127Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
128Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
129Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
130Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
131Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
132Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai.
133Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
134A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
135Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
136Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
137Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
138Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
139Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
140A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
141Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
142Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
143To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
144Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
145Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
146Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
147Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
148Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
149Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
150Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
151To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
152"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
153Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
154Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)?
155Shin, bã ku tunãni?
156Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
157To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
158Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
159Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
160Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
161To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
162Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
163Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
164"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,[1] fãce yanã da matsayi sananne."
165"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
166"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
167Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
168"Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
169"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
170Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
171Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
172Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
173Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
174Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
175Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.[1]
176Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
177To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
178Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
179Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
180Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
181Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
182Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.