الأعلى
The Most High • 19 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
2Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
3Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
4Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
5Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
6Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
7Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
8Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
9Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
10Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
11Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
12Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
13Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
14Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
15Kuma ya ambaci sũnan[1] Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
16Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.[1]
17Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
18Lalle ne, wannan[1] yanã a cikin littafan farko.
19Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.