Al-Ghashiyah

الغاشية

The Overwhelming26 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَةِ﴿١

1Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ﴿٢

2Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.

عَامِلَةٞ نَّاصِبَةٞ﴿٣

3Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.

تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِيَةٗ﴿٤

4Zã su shiga wata wuta mai zãfi.

تُسۡقَىٰ مِنۡ عَيۡنٍ ءَانِيَةٖ﴿٥

5Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.

لَّيۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٖ﴿٦

6Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.

لَّا يُسۡمِنُ وَلَا يُغۡنِي مِن جُوعٖ﴿٧

7Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاعِمَةٞ﴿٨

8Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.

لِّسَعۡيِهَا رَاضِيَةٞ﴿٩

9Game da aikinsu, masu yarda ne.

فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ﴿١٠

10(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.

لَّا تَسۡمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةٗ﴿١١

11Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.

فِيهَا عَيۡنٞ جَارِيَةٞ﴿١٢

12A cikinta akwai marmaro mai gudãna.

فِيهَا سُرُرٞ مَّرۡفُوعَةٞ﴿١٣

13A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.

وَأَكۡوَابٞ مَّوۡضُوعَةٞ﴿١٤

14Da kõfuna ar'aje.

وَنَمَارِقُ مَصۡفُوفَةٞ﴿١٥

15Da filõli[1] jẽre,

وَزَرَابِيُّ مَبۡثُوثَةٌ﴿١٦

16Da katifu shimfiɗe.

أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلۡإِبِلِ كَيۡفَ خُلِقَتۡ﴿١٧

17Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?

وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ رُفِعَتۡ﴿١٨

18Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?

وَإِلَى ٱلۡجِبَالِ كَيۡفَ نُصِبَتۡ﴿١٩

19Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?

وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَيۡفَ سُطِحَتۡ﴿٢٠

20Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?

فَذَكِّرۡ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٞ﴿٢١

21sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.

لَّسۡتَ عَلَيۡهِم بِمُصَيۡطِرٍ﴿٢٢

22Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.

إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ﴿٢٣

23Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.

فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَكۡبَرَ﴿٢٤

24To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.

إِنَّ إِلَيۡنَآ إِيَابَهُمۡ﴿٢٥

25Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.

ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا حِسَابَهُم﴿٢٦

26Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.

RELATED SURAHS