Al-Balad

البلد

The City20 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ﴿١

1Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari[1] ba.

وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ﴿٢

2Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.

وَوَالِدٖ وَمَا وَلَدَ﴿٣

3Da mahaifi da abin da ya haifa.

لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِي كَبَدٍ﴿٤

4Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.

أَيَحۡسَبُ أَن لَّن يَقۡدِرَ عَلَيۡهِ أَحَدٞ﴿٥

5Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?

يَقُولُ أَهۡلَكۡتُ مَالٗا لُّبَدًا﴿٦

6Yana cẽwa "Na[1] halakarda dũkiya mai yawa,"

أَيَحۡسَبُ أَن لَّمۡ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ﴿٧

7Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?

أَلَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ عَيۡنَيۡنِ﴿٨

8Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?

وَلِسَانٗا وَشَفَتَيۡنِ﴿٩

9Da harshe, da leɓɓa biyu.

وَهَدَيۡنَٰهُ ٱلنَّجۡدَيۡنِ﴿١٠

10Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi[1] biyu ba?

فَلَا ٱقۡتَحَمَ ٱلۡعَقَبَةَ﴿١١

11To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡعَقَبَةُ﴿١٢

12Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?

فَكُّ رَقَبَةٍ﴿١٣

13Ita ce fansar wuyan bãwa.

أَوۡ إِطۡعَٰمٞ فِي يَوۡمٖ ذِي مَسۡغَبَةٖ﴿١٤

14Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.

يَتِيمٗا ذَا مَقۡرَبَةٍ﴿١٥

15Ga marãya ma'abũcin zumunta.

أَوۡ مِسۡكِينٗا ذَا مَتۡرَبَةٖ﴿١٦

16Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.

ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡمَرۡحَمَةِ﴿١٧

17Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.

أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ﴿١٨

18Waɗannan ne ma'abũta albarka[1]

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ﴿١٩

19Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci[1]

عَلَيۡهِمۡ نَارٞ مُّؤۡصَدَةُۢ﴿٢٠

20A kansu akwai wata wuta abar kullewa.

RELATED SURAHS