المدثر
The Cloaked One • 56 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
2Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
3Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
4Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
5Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
6Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
7Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
8To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
9To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
10A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
11Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
12Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
13Da ɗiyã halartattu,
14Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
15Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
16Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai.
17Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
18Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)
19Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.
20Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.
21Sa'an nan, ya yi tunãni
22Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.
23Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,
24Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."
25"Wannan maganar mutum dai ce."
26Zã Ni ƙõna shi da Saƙar.
27Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!
28Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.
29Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).
30A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.
31Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.
32A'aha! Ina rantsuwa da watã.
33Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya.
34Da sãfiya idan ta wãye.
35Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.
36Mai gargaɗĩ ce ga mutum.
37Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.
38Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.
39Fãce mutãnen dãma.
40A cikin Aljanna suna tambayar jũna.
41Game da mãsu laifi.
42(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"
43Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."
44"Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."
45"Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."
46"Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."
47"Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."
48Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
49Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
50Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
51Sun gudu daga zãki.
52A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
53A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
54A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.
55Dõmin wanda ya so, ya tuna.
56Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.