Al-Qiyamah

القيامة

The Resurrection40 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ﴿١

1Bã sai Nã yi rantsuwa[1] da Rãnar ¡iyãma ba.

وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ﴿٢

2Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin[1] kansa ba.

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ﴿٣

3Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ﴿٤

4Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ﴿٥

5Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ﴿٦

6Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ﴿٧

7To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ﴿٨

8Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ﴿٩

9Aka tãra rãnã da watã

يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ﴿١٠

10Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"

كَلَّا لَا وَزَرَ﴿١١

11A'aha! bãbu mafaka.

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ﴿١٢

12zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ﴿١٣

13Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ﴿١٤

14Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ﴿١٥

15Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ﴿١٦

16Kada ka mõtsar[1] da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).

إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ﴿١٧

17Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ﴿١٨

18To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ﴿١٩

19sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.

كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ﴿٢٠

20A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.

وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ﴿٢١

21Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ﴿٢٢

22Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ﴿٢٣

23Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ﴿٢٤

24Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.

تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ﴿٢٥

25Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.

كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ﴿٢٦

26A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.

وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ﴿٢٧

27kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"

وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ﴿٢٨

28Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.

وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ﴿٢٩

29Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ﴿٣٠

30Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa[1] take.

فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ﴿٣١

31To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ﴿٣٢

32Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ﴿٣٣

33Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ﴿٣٤

34Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ﴿٣٥

35Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى﴿٣٦

36Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ﴿٣٧

37Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ﴿٣٨

38Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ﴿٣٩

39Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ﴿٤٠

40Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?[1]

RELATED SURAHS