Al-Mursalat

المرسلات

Those Sent Forth50 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا﴿١

1Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.

فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا﴿٢

2Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.

وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا﴿٣

3Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.

فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا﴿٤

4sa'an nan, da ãyõyi[1] mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.

فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا﴿٥

5Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.

عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا﴿٦

6Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.

إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ﴿٧

7Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ﴿٨

8To, idan taurãri aka shãfe haskensu.

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ﴿٩

9Kuma, idan sama aka tsãge ta.

وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ﴿١٠

10Kuma, idan duwãtsu aka nike su.

وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ﴿١١

11Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.

لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ﴿١٢

12Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.

لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ﴿١٣

13Domin rãnar rarrabẽwa.[1]

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ﴿١٤

14Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿١٥

15Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿١٦

16Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.

ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ﴿١٧

17Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?

كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ﴿١٨

18Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿١٩

19Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ﴿٢٠

20Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.

فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٖ مَّكِينٍ﴿٢١

21Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.

إِلَىٰ قَدَرٖ مَّعۡلُومٖ﴿٢٢

22Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.

فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ﴿٢٣

23Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٢٤

24Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا﴿٢٥

25Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.

أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا﴿٢٦

26Ga rãyayyu da matattu,

وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا﴿٢٧

27Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٢٨

28Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ﴿٢٩

29Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!

ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلّٖ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٖ﴿٣٠

30Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.

لَّا ظَلِيلٖ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ﴿٣١

31Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.

إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٖ كَٱلۡقَصۡرِ﴿٣٢

32Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.

كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٞ صُفۡرٞ﴿٣٣

33Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٣٤

34Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ﴿٣٥

35Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.

وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ﴿٣٦

36Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٣٧

37Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ﴿٣٨

38Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.

فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٞ فَكِيدُونِ﴿٣٩

39To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٤٠

40Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ﴿٤١

41Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.

وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ﴿٤٢

42Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.

كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ﴿٤٣

43(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ﴿٤٤

44Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٤٥

45Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ﴿٤٦

46(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٤٧

47Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ﴿٤٨

48Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ﴿٤٩

49Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ﴿٥٠

50To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni

RELATED SURAHS