النبأ
The Tidings • 40 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1A kan mẽ suke tambayar jũna?
2A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
3Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
4A'aha! Zã su sani.
5Kuma, a'aha! Zã su sani.
6Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
7Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
8Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
9Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
10Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
11Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
12Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
13Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
14Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
15Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
16Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
17Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
18Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
19Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
20Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
21Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
22Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
23Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
24Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
25Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
26Sakamako mai dãcẽwa.
27Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
28Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa!
29Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
30Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
31Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
32Lambuna da inabõbi.
33Da yan Mata tsaraikun Juna
34Da hinjãlan giya cikakku.
35Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
36Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
37Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
38Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
39Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
40Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"