القلم
The Pen • 52 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
2Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
3Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
4Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
5Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
6Ga wanenku haukã take.
7Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
8Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
9Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
10Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
11Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
12Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
13Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri).
14Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
15Idan ana karanta masa ãyõyin Mu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
16Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
17Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
18Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
19Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
20Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
21Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
22Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
23Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
24"Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
25Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
26Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
27"Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
28Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
29Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
30Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
31Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
32"Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
33Haka dai azãbar[1] take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
34Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
35Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
36Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
37Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
38Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
39Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
40Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
41Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
42Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba.
43Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
44Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
45Ina jinkirtã musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne.
46Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
47Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
48Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
49Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
50Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
51Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
52Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.