Al-Humazah

الهمزة

The Gossipmonger9 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَيۡلٞ لِّكُلِّ هُمَزَةٖ لُّمَزَةٍ﴿١

1Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).

ٱلَّذِي جَمَعَ مَالٗا وَعَدَّدَهُۥ﴿٢

2Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.

يَحۡسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخۡلَدَهُۥ﴿٣

3Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.

كَلَّاۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِي ٱلۡحُطَمَةِ﴿٤

4A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحُطَمَةُ﴿٥

5Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?

نَارُ ٱللَّهِ ٱلۡمُوقَدَةُ﴿٦

6Wutar Allah ce wadda ake hurawa.

ٱلَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى ٱلۡأَفۡـِٔدَةِ﴿٧

7Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.

إِنَّهَا عَلَيۡهِم مُّؤۡصَدَةٞ﴿٨

8Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu.

فِي عَمَدٖ مُّمَدَّدَةِۭ﴿٩

9A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.

RELATED SURAHS