الفيل
The Elephant • 5 ayahs • Meccan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa[1] ba?
2Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba?
3Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
4Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
5Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?