Al-Ma'arij

المعارج

The Ascending Stairways44 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

سَأَلَ سَآئِلُۢ بِعَذَابٖ وَاقِعٖ﴿١

1Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.

لِّلۡكَٰفِرِينَ لَيۡسَ لَهُۥ دَافِعٞ﴿٢

2Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.

مِّنَ ٱللَّهِ ذِي ٱلۡمَعَارِجِ﴿٣

3Daga Allah Mai matãkala.

تَعۡرُجُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥ خَمۡسِينَ أَلۡفَ سَنَةٖ﴿٤

4Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.

فَٱصۡبِرۡ صَبۡرٗا جَمِيلًا﴿٥

5Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.

إِنَّهُمۡ يَرَوۡنَهُۥ بَعِيدٗا﴿٦

6Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.

وَنَرَىٰهُ قَرِيبٗا﴿٧

7Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.

يَوۡمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلۡمُهۡلِ﴿٨

8Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.

وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ﴿٩

9Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.

وَلَا يَسۡـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمٗا﴿١٠

10Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.

يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ﴿١١

11Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ﴿١٢

12Da matarsa da ɗan'uwansa.

وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِي تُـٔۡوِيهِ﴿١٣

13Da danginsa, mãsu tattarã shi.

وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ يُنجِيهِ﴿١٤

14Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.

كَلَّآۖ إِنَّهَا لَظَىٰ﴿١٥

15A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,

نَزَّاعَةٗ لِّلشَّوَىٰ﴿١٦

16Mai twãle fãtar goshi.

تَدۡعُواْ مَنۡ أَدۡبَرَ وَتَوَلَّىٰ﴿١٧

17Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.

وَجَمَعَ فَأَوۡعَىٰٓ﴿١٨

18Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.

۞ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا﴿١٩

19Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.

إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعٗا﴿٢٠

20Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.

وَإِذَا مَسَّهُ ٱلۡخَيۡرُ مَنُوعًا﴿٢١

21Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.

إِلَّا ٱلۡمُصَلِّينَ﴿٢٢

22Sai mãsu yin salla,

ٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ دَآئِمُونَ﴿٢٣

23Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.

وَٱلَّذِينَ فِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ مَّعۡلُومٞ﴿٢٤

24Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.

لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ﴿٢٥

25Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.

وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ﴿٢٦

26Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.

وَٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ﴿٢٧

27Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.

إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمۡ غَيۡرُ مَأۡمُونٖ﴿٢٨

28Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ﴿٢٩

29Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.

إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ﴿٣٠

30Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.

فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ﴿٣١

31To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ﴿٣٢

32Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.

وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَٰدَٰتِهِمۡ قَآئِمُونَ﴿٣٣

33Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.

وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ﴿٣٤

34Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.

أُوْلَٰٓئِكَ فِي جَنَّٰتٖ مُّكۡرَمُونَ﴿٣٥

35Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne

فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قِبَلَكَ مُهۡطِعِينَ﴿٣٦

36Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).

عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ﴿٣٧

37Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!

أَيَطۡمَعُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُدۡخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٖ﴿٣٨

38Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?

كَلَّآۖ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّمَّا يَعۡلَمُونَ﴿٣٩

39A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.

فَلَآ أُقۡسِمُ بِرَبِّ ٱلۡمَشَٰرِقِ وَٱلۡمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ﴿٤٠

40Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ﴿٤١

41Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.

فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ﴿٤٢

42Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).

يَوۡمَ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ سِرَاعٗا كَأَنَّهُمۡ إِلَىٰ نُصُبٖ يُوفِضُونَ﴿٤٣

43Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.

خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۚ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ﴿٤٤

44Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)

RELATED SURAHS