النصر
The Divine Support • 3 ayahs • Medinan
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.
2Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya.
3To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne.