Ash-Shu'ara

الشعراء

The Poets227 ayahsMeccan

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

طسٓمٓ﴿١

1T. S̃. M̃.

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ﴿٢

2Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.

لَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ﴿٣

3Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba! [1]

إِن نَّشَأۡ نُنَزِّلۡ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةٗ فَظَلَّتۡ أَعۡنَٰقُهُمۡ لَهَا خَٰضِعِينَ﴿٤

4Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.

وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٖ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ مُحۡدَثٍ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهُ مُعۡرِضِينَ﴿٥

5Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.

فَقَدۡ كَذَّبُواْ فَسَيَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ﴿٦

6To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَمۡ أَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ﴿٧

7Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿٨

8Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿٩

9Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.

وَإِذۡ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئۡتِ ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ﴿١٠

10Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.

قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَۚ أَلَا يَتَّقُونَ﴿١١

11"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"

قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ﴿١٢

12Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.

وَيَضِيقُ صَدۡرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرۡسِلۡ إِلَىٰ هَٰرُونَ﴿١٣

13"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci[1] kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.

وَلَهُمۡ عَلَيَّ ذَنۢبٞ فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ﴿١٤

14"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."

قَالَ كَلَّاۖ فَٱذۡهَبَا بِـَٔايَٰتِنَآۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسۡتَمِعُونَ﴿١٥

15Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."

فَأۡتِيَا فِرۡعَوۡنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٦

16"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."

أَنۡ أَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ﴿١٧

17"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."

قَالَ أَلَمۡ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدٗا وَلَبِثۡتَ فِينَا مِنۡ عُمُرِكَ سِنِينَ﴿١٨

18Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"

وَفَعَلۡتَ فَعۡلَتَكَ ٱلَّتِي فَعَلۡتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ﴿١٩

19"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"

قَالَ فَعَلۡتُهَآ إِذٗا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ﴿٢٠

20Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi."

فَفَرَرۡتُ مِنكُمۡ لَمَّا خِفۡتُكُمۡ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكۡمٗا وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ﴿٢١

21"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."

وَتِلۡكَ نِعۡمَةٞ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنۡ عَبَّدتَّ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ﴿٢٢

22"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."

قَالَ فِرۡعَوۡنُ وَمَا رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿٢٣

23Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"

قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ﴿٢٤

24Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."

قَالَ لِمَنۡ حَوۡلَهُۥٓ أَلَا تَسۡتَمِعُونَ﴿٢٥

25Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"

قَالَ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿٢٦

26Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."

قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِيٓ أُرۡسِلَ إِلَيۡكُمۡ لَمَجۡنُونٞ﴿٢٧

27Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."

قَالَ رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡقِلُونَ﴿٢٨

28Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."

قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذۡتَ إِلَٰهًا غَيۡرِي لَأَجۡعَلَنَّكَ مِنَ ٱلۡمَسۡجُونِينَ﴿٢٩

29Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."

قَالَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكَ بِشَيۡءٖ مُّبِينٖ﴿٣٠

30Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"

قَالَ فَأۡتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ﴿٣١

31Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."

فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ﴿٣٢

32Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.

وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّٰظِرِينَ﴿٣٣

33Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.

قَالَ لِلۡمَلَإِ حَوۡلَهُۥٓ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ﴿٣٤

34(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!

يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِۦ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ﴿٣٥

35"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"

قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَٱبۡعَثۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ﴿٣٦

36Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."

يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٖ﴿٣٧

37"Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."

فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ﴿٣٨

38Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.

وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلۡ أَنتُم مُّجۡتَمِعُونَ﴿٣٩

39Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?

لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ﴿٤٠

40"Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُواْ لِفِرۡعَوۡنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ﴿٤١

41To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"

قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ﴿٤٢

42Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."

قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ﴿٤٣

43Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."

فَأَلۡقَوۡاْ حِبَالَهُمۡ وَعِصِيَّهُمۡ وَقَالُواْ بِعِزَّةِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبُونَ﴿٤٤

44Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."

فَأَلۡقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ﴿٤٥

45Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.

فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ﴿٤٦

46Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.

قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿٤٧

47Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."

رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ﴿٤٨

48"Ubangijin Mũsa da Hãrũna."

قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَ فَلَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٖ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ﴿٤٩

49Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."

قَالُواْ لَا ضَيۡرَۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ﴿٥٠

50Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."

إِنَّا نَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ﴿٥١

51"Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."

۞ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِيٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ﴿٥٢

52Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã[1] ne.

فَأَرۡسَلَ فِرۡعَوۡنُ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ﴿٥٣

53Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.

إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَشِرۡذِمَةٞ قَلِيلُونَ﴿٥٤

54"Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."

وَإِنَّهُمۡ لَنَا لَغَآئِظُونَ﴿٥٥

55"Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."

وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ﴿٥٦

56"Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."

فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ﴿٥٧

57Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.

وَكُنُوزٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ﴿٥٨

58Da taskõki da mazauni mai kyau.

كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ﴿٥٩

59Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.

فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ﴿٦٠

60Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.

فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلۡجَمۡعَانِ قَالَ أَصۡحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدۡرَكُونَ﴿٦١

61Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."

قَالَ كَلَّآۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهۡدِينِ﴿٦٢

62Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."

فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٖ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ﴿٦٣

63Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,[1] kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.

وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ﴿٦٤

64Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.

وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ﴿٦٥

65Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.

ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ﴿٦٦

66Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿٦٧

67Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿٦٨

68Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.

وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ إِبۡرَٰهِيمَ﴿٦٩

69Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا تَعۡبُدُونَ﴿٧٠

70A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"

قَالُواْ نَعۡبُدُ أَصۡنَامٗا فَنَظَلُّ لَهَا عَٰكِفِينَ﴿٧١

71Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."

قَالَ هَلۡ يَسۡمَعُونَكُمۡ إِذۡ تَدۡعُونَ﴿٧٢

72Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"

أَوۡ يَنفَعُونَكُمۡ أَوۡ يَضُرُّونَ﴿٧٣

73"Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"

قَالُواْ بَلۡ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ﴿٧٤

74Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."

قَالَ أَفَرَءَيۡتُم مَّا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ﴿٧٥

75Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"

أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلۡأَقۡدَمُونَ﴿٧٦

76"Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"

فَإِنَّهُمۡ عَدُوّٞ لِّيٓ إِلَّا رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿٧٧

77"To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."

ٱلَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهۡدِينِ﴿٧٨

78"Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."

وَٱلَّذِي هُوَ يُطۡعِمُنِي وَيَسۡقِينِ﴿٧٩

79"Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."

وَإِذَا مَرِضۡتُ فَهُوَ يَشۡفِينِ﴿٨٠

80"Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."

وَٱلَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحۡيِينِ﴿٨١

81"Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."

وَٱلَّذِيٓ أَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لِي خَطِيٓـَٔتِي يَوۡمَ ٱلدِّينِ﴿٨٢

82"Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."

رَبِّ هَبۡ لِي حُكۡمٗا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّٰلِحِينَ﴿٨٣

83"Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."

وَٱجۡعَل لِّي لِسَانَ صِدۡقٖ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ﴿٨٤

84"Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya[1] a cikin mutãnen ƙarshe."

وَٱجۡعَلۡنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ﴿٨٥

85"Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."

وَٱغۡفِرۡ لِأَبِيٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ﴿٨٦

86"Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."

وَلَا تُخۡزِنِي يَوۡمَ يُبۡعَثُونَ﴿٨٧

87"Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."

يَوۡمَ لَا يَنفَعُ مَالٞ وَلَا بَنُونَ﴿٨٨

88"A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."

إِلَّا مَنۡ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلۡبٖ سَلِيمٖ﴿٨٩

89"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."

وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ﴿٩٠

90Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.

وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِلۡغَاوِينَ﴿٩١

91Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.

وَقِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ﴿٩٢

92Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"

مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلۡ يَنصُرُونَكُمۡ أَوۡ يَنتَصِرُونَ﴿٩٣

93"Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"

فَكُبۡكِبُواْ فِيهَا هُمۡ وَٱلۡغَاوُۥنَ﴿٩٤

94Sai aka kikkife su[1] a cikinta, su da halakakkun.

وَجُنُودُ إِبۡلِيسَ أَجۡمَعُونَ﴿٩٥

95Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.

قَالُواْ وَهُمۡ فِيهَا يَخۡتَصِمُونَ﴿٩٦

96Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,

تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ﴿٩٧

97"Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."

إِذۡ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿٩٨

98"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.

وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلۡمُجۡرِمُونَ﴿٩٩

99"Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."

فَمَا لَنَا مِن شَٰفِعِينَ﴿١٠٠

100"Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."

وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٖ﴿١٠١

101"Kuma bã mu da abõki, masõyi."

فَلَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ﴿١٠٢

102"Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿١٠٣

103Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿١٠٤

104Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ نُوحٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ﴿١٠٥

105Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ﴿١٠٦

106A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba?"

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ﴿١٠٧

107"Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٠٨

108"To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٠٩

109"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١١٠

110"Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

۞ قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلۡأَرۡذَلُونَ﴿١١١

111Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"

قَالَ وَمَا عِلۡمِي بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ﴿١١٢

112Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."

إِنۡ حِسَابُهُمۡ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّيۖ لَوۡ تَشۡعُرُونَ﴿١١٣

113"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."

وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ﴿١١٤

114"Ban zama mai kõre mũminai ba."

إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ﴿١١٥

115"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."

قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمَرۡجُومِينَ﴿١١٦

116Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"

قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوۡمِي كَذَّبُونِ﴿١١٧

117Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."

فَٱفۡتَحۡ بَيۡنِي وَبَيۡنَهُمۡ فَتۡحٗا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ﴿١١٨

118"Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ﴿١١٩

119Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.

ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ﴿١٢٠

120Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿١٢١

121Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿١٢٢

122Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.

كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ﴿١٢٣

123Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ﴿١٢٤

124A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ﴿١٢٥

125"Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٢٦

126"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٢٧

127"Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."

أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةٗ تَعۡبَثُونَ﴿١٢٨

128"Shin, kunã yin ginin sitadiyo[1] a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"

وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ﴿١٢٩

129"Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?[1]"

وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ﴿١٣٠

130"Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٣١

131"To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ﴿١٣٢

132"Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."

أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٖ وَبَنِينَ﴿١٣٣

133"Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."

وَجَنَّٰتٖ وَعُيُونٍ﴿١٣٤

134"Da gõnaki da marẽmari."

إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ﴿١٣٥

135"Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."

قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ﴿١٣٦

136Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."

إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿١٣٧

137"Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen[1] mutãnen farko."

وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ﴿١٣٨

138"Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."

فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿١٣٩

139Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿١٤٠

140Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ﴿١٤١

141Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ﴿١٤٢

142A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ﴿١٤٣

143"Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٤٤

144"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٤٥

145"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."

أَتُتۡرَكُونَ فِي مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ﴿١٤٦

146"Shin, anã barin ku[1] a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"

فِي جَنَّٰتٖ وَعُيُونٖ﴿١٤٧

147"A cikin gõnaki da marẽmari."

وَزُرُوعٖ وَنَخۡلٖ طَلۡعُهَا هَضِيمٞ﴿١٤٨

148"Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi[1] mãsu narkẽwa a ciki?"

وَتَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا فَٰرِهِينَ﴿١٤٩

149"Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٥٠

150"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

وَلَا تُطِيعُوٓاْ أَمۡرَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ﴿١٥١

151"Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."

ٱلَّذِينَ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ﴿١٥٢

152"Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."

قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ﴿١٥٣

153Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."

مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا فَأۡتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ﴿١٥٤

154"Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٞ لَّهَا شِرۡبٞ وَلَكُمۡ شِرۡبُ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ﴿١٥٥

155Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan[1] yini, kuma kunã da shan yini sasanne."

وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٖ﴿١٥٦

156"Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."

فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ﴿١٥٧

157Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.

فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿١٥٨

158Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿١٥٩

159Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ﴿١٦٠

160Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ﴿١٦١

161A lõkacin da ɗan'uwansu,[1] Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ﴿١٦٢

162"Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٦٣

163"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٦٤

164"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

أَتَأۡتُونَ ٱلذُّكۡرَانَ مِنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٦٥

165"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"

وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٌ عَادُونَ﴿١٦٦

166"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"

قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُخۡرَجِينَ﴿١٦٧

167Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."

قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلۡقَالِينَ﴿١٦٨

168Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."

رَبِّ نَجِّنِي وَأَهۡلِي مِمَّا يَعۡمَلُونَ﴿١٦٩

169"Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."

فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ﴿١٧٠

170Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.

إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ﴿١٧١

171Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.

ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ﴿١٧٢

172Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu.

وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ﴿١٧٣

173Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿١٧٤

174Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿١٧٥

175Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ﴿١٧٦

176Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ شُعَيۡبٌ أَلَا تَتَّقُونَ﴿١٧٧

177A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ﴿١٧٨

178"Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ﴿١٧٩

179"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٨٠

180"Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

۞ أَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُخۡسِرِينَ﴿١٨١

181"Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."

وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ﴿١٨٢

182"Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."

وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ﴿١٨٣

183"Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."

وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلۡجِبِلَّةَ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿١٨٤

184"Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."

قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ﴿١٨٥

185Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."

وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ﴿١٨٦

186"Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."

فَأَسۡقِطۡ عَلَيۡنَا كِسَفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ﴿١٨٧

187"To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."

قَالَ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَا تَعۡمَلُونَ﴿١٨٨

188Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."

فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ﴿١٨٩

189Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije[1] ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ﴿١٩٠

190Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ﴿١٩١

191Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ﴿١٩٢

192Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.

نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ﴿١٩٣

193Rũhi[1] amintacce ne ya sauka da shi.

عَلَىٰ قَلۡبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ﴿١٩٤

194A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.

بِلِسَانٍ عَرَبِيّٖ مُّبِينٖ﴿١٩٥

195Da harshe na Larabci mai bayãni.

وَإِنَّهُۥ لَفِي زُبُرِ ٱلۡأَوَّلِينَ﴿١٩٦

196Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.

أَوَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ ءَايَةً أَن يَعۡلَمَهُۥ عُلَمَٰٓؤُاْ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ﴿١٩٧

197Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?

وَلَوۡ نَزَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ بَعۡضِ ٱلۡأَعۡجَمِينَ﴿١٩٨

198Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,

فَقَرَأَهُۥ عَلَيۡهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ مُؤۡمِنِينَ﴿١٩٩

199Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.

كَذَٰلِكَ سَلَكۡنَٰهُ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ﴿٢٠٠

200Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.

لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ﴿٢٠١

201Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.

فَيَأۡتِيَهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ﴿٢٠٢

202Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.

فَيَقُولُواْ هَلۡ نَحۡنُ مُنظَرُونَ﴿٢٠٣

203Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"

أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ﴿٢٠٤

204Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa?

أَفَرَءَيۡتَ إِن مَّتَّعۡنَٰهُمۡ سِنِينَ﴿٢٠٥

205Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,

ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُواْ يُوعَدُونَ﴿٢٠٦

206Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,

مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يُمَتَّعُونَ﴿٢٠٧

207Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare[1] su.

وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ﴿٢٠٨

208Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.

ذِكۡرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَٰلِمِينَ﴿٢٠٩

209Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.

وَمَا تَنَزَّلَتۡ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ﴿٢١٠

210Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.

وَمَا يَنۢبَغِي لَهُمۡ وَمَا يَسۡتَطِيعُونَ﴿٢١١

211Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.

إِنَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّمۡعِ لَمَعۡزُولُونَ﴿٢١٢

212Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.

فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ﴿٢١٣

213Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.

وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ﴿٢١٤

214Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.

وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ﴿٢١٥

215Kuma ka sassauta fikãfikanka[1] ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.

فَإِنۡ عَصَوۡكَ فَقُلۡ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ﴿٢١٦

216Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ﴿٢١٧

217Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ﴿٢١٨

218Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.

وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّٰجِدِينَ﴿٢١٩

219Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.

إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ﴿٢٢٠

220Lalle Shi, Shi[1] ne Mai ji, Masani.

هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ﴿٢٢١

221Shin, (kunã so) in gaya[1] muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?

تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ﴿٢٢٢

222Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.

يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ﴿٢٢٣

223Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.

وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ﴿٢٢٤

224Kuma mawãƙa[1] halakakku ne ke bin su.

أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِي كُلِّ وَادٖ يَهِيمُونَ﴿٢٢٥

225Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?

وَأَنَّهُمۡ يَقُولُونَ مَا لَا يَفۡعَلُونَ﴿٢٢٦

226Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَذَكَرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱنتَصَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَيَّ مُنقَلَبٖ يَنقَلِبُونَ﴿٢٢٧

227Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.

RELATED SURAHS